Ba ni da wani abin ɓoyewa, Malami ya shaida wa ‘yan majalisar wakilai a kan binciken sayar da man dala biliyan 2.4 ba bisa ƙa’ida ba.
Daga Hassan Abubakar Ahmad Magini II
Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya sake bayyana cewa bai san wani abu da ake zargin an sayar da ganga miliyan 48 na ɗanyen man fetur ba bisa ƙa’ida ba wanda ya kai dala biliyan 2.4.
Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya gurfana gaban kwamitin adhoc na Majalisar Wakilai da ke binciken zargin asarar sama da dala biliyan 2.4 na kuɗaɗen shiga daga sayar da ganga miliyan 48 na danyen mai da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a shekarar 2015 da suka haɗa da duk wani danyen mai da ake fitarwa da kuma sayar da shi daga shekarar 2014 har zuwa yau ƙarƙashin jagorancin. Hon. Mark Gbillah.
Malami dai ya taɓa bayyana a gaban kwamitin adhoc na Majalisar Wakilai da ke binciken asarar da aka yi a shekarar 2015, da suka haɗa da fitar da ɗanyen mai daga 2014 har zuwa wata guda da ya gabata, ya bayyana zargin a matsayin mara tushe kuma ba shi da tushe.
Add Comment