Addini Labarai

Ba Ni Da Kudin Sayen Littattafai, Harkokina Sun Tsaya Cak – Sheik Abduljabbar

Malamin addinin Musuluncin nan da Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar a gaban kotu kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W), Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara, ya ce a yanzu ba shi da kudin sayen littattafai sakamakon tsayawar harkokinsa cak, tun lokacin da aka tsare shi a kurkuku.

Ya bayyana hakan ne a gaban kotun Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano ranar Alhamis, yayin da aka dawo ci gaba da sauraron kararsa.

Yana magana ne lokacin da kotun ta umarce shi da ya sayi litattafan Hadisan Sahihu Muslim da Sahihul Bukhari wadanda ba su da sharhi ko fassara a ciki, kamar yadda ya bukaci a bashi su, inda shi kuma ya shaida wa kotun cewa ba shi da kudin saye.

Ba ni da kudin da zan iya sayen litattafan hadisan nan guda biyu saboda tunda aka tsare ni a gidan gyaran hali tsawon watanni biyar, harkokina suka tsaya cak,” inji shi.

Anan ne Daraktar Shigar da Kara ta Gwamnatin Jihar kano Barista Aisha Mahmood, ta dauki alkawarin cewa Gwamnatin Kano za ta ba wanda ake kara kudin da zai sayi litattafan kafin nan da ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamban 2021.

Kotun ta ce za a saya masa littattafan ne domin ya sami damar yin tambayoyi ga shaidar da bangaren masu kara suka gabatar a gaban kotun.

Idan za a iya tunawa, Gwamantin Jihar Kano ce ta yi karar malamin gaban kotun bisa tuhumarsa da laifukan yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Tun da farko,  lauyoyin da ke gabatar da kara karkashin jagorancin Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN), sun sake gabatar wa kotu shaidarsu na biyu, mai suna Murtala Kabir Muhammad  wanda mazaunin unguwar Kofar Na’isa, Lokon Makera ne, wanda kuma dalibin Malam Abduljabbar ne, domin ya amsa tambayoyi.

Sai dai lokacin da aka ba wanda ake kara damar yin tambayoyi ga shaida na biyu,  sai ya fara yin amfani da wani littafi, inda yake budawa yana karanta tambayoyi ga shaidar.

Hakan ya sa lauyoyin masu kara suka yi suka akai, inda suka ce littafin da Abduljabbar din yake amfani da shi wajen yin tambayoyi ba shi ne wanda shaidarsu ya ce ya duba ba.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.