Labarai

Ba Ni Aka Yi Wa Sujjada Ba, Sallah Suke Yi, Cewar Sarki Sanusi II

Daga Muhammad Usman Gashua
Ga fassarar bayanan da jaridar Daily Nigerian ta wallafa daga harshen Turanci zuwa Hausa.
Sarkin Kano mai murabus Muhammadu Sanusi II, yayi bayani akan hototon da ya haifar da ce-ce-ku-ce, wanda yake nuna mutane guda biyu suna sujada agabansa.

Sarki Muhammad Sanusi wanda a baya-bayan nan aka nada a mukamin Khalifan Tijjaniyya na Nigeria, ya tsinci kansa cikin surutan yan social media dalilin wannan hoto.

A yayin da wasu ke Allah wadai da aikin mutane biyu da suke sujadar a gabansa, wasu sun zargi Sarkin da basu damar yin hakan.

Amma a tattaunawar sa ta wayar tarho da gidan jaridar “DAILY NIGERIAN” Sarkin yace ” wannan Sujadar ta sallace ba ta gaisuwa bace a gareshi”.

Ya kara da cewa ” Hoton an dauke shi ne ayayin daya daga cikin karatunsa na littafin Madarijus Salikin, wanda ake farawa karfe 04:15 bayan Sallar la’asar ”

Yace ” abisa ka’ida nakan fitowa karfe 04:00pm domin na jagoranci sallar la’asar, wanda bayan sallar ne muke fara kararunmu na littafin Madaarijus Salikin da misalin karfe 04:15.

“Wadannan mutane guda biyun da suka zamto ababen zargi (agare ni), sunzo Sallar la’asar dinne a makare, ayayin da ni na mike domin hawa kan kujerata, sai daya daga cikin mahalarta ya dauki wannan hoto, ayayin da su kuma suke hali na Sujada, idan kuka lura da kyau, zakuga Darduma wacce nayi sallah akanta, babu ta yadda zan kyale, ko na karfafi mutane su gurfana a irin wannan yanayi a gabana”.

DA A CE MUTANE SUN KASANCE MASU BIN DIDDIGIN BATU GAME DA DUK LABARIN DA YAZO MUSU, KAMAR YADDA ALLAH YAYI UMARNI CIKIN FADINSA

يا أيها الذين آمنوا إن جاءكم فاسق بنبأ فتبينوا أن تصيبوا قوما بجهالة فتصبحوا على ما فعلتم نادمين

TO DA BA’AZO GA IRIN WANNAN MATAKI DA ZA’A KE KIRKIRAR LABARIN KARYA ANA JINGINAWA BAWAN ALLAH, KAWAI SABODA KIYAYYAR DA AKE NUNA MASA.

YANZU ME AMFANIN YADA LABARIN KARYA ALHAKI GASHI GASKIYAR TA BAYYANA?

ALLAH SHI KYAUTA.

ALHAMDULILLAH.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: