Siyasa

Ba mu yarda Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 ba -inji Matasan jam’iyyar APC

Daga Alfijir

Bai kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara a shekarar 2019 ba, a cewar wata kungiyar matsan jami’yyar APC.

Shugaban kungiyar ‘yan-ganin-kashenin Buhari (Buhari Diehard Supporters) Mustapha Panandas ya bayyana haka ne a matsayin martani game da ikirarin da ministar harkokin mata Aisha Alhassan ta yi na goyon bayan tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar.

 

Mustapha Panandas ya ce duk da suna matukar son Muhammadu Buhari, nazarinsu ya nuna musu cewa idan ya sake fitowa takara zai sha kaye saboda akwai ministoci da jami’an gwamnati da dama wadanda za su yaki tafiyar.

Ya shaidawa alfijir.com cewa dama can sun san haka za ta faru kasancewar Muhammadu Buhari ba ya tafiya da mutanen da suka wahalta masa a cikin gwamnatinsa, sai ‘yan miya ta yi dadi.

Panandas, wanda ya ce suna tare da Buhari tun 2003, ya bada misali da irinsu marigayi Garba Gadi, Almajiri Gaidam da Naja’atu Bala Mohammed, wadanda ya ce duk sun yi wa shugaba Muhammadu Buhari wahala a siyasance amma ba’a yi da su.

Sai dai shugaban kungiyar ‘yan-gani-kashenin-Buhari ya ce akwai matakin da shugaban kasar zai iya dauka kafin karshen 2017 domin kyautata shirin takararsa ta gaba.

“Shawarata ga shugaba Muhammadu Buhari, duk yadda ya kai ga son ya kyautatawa talaka, in bada shi da mukarrabai nagari babu inda za shi.”

“Tun da wadannan an ba su dama sun gaza, sai a sallame su a nemo wadanda za su iya.”