Darajar kasuwar hannayen jari a Nijeriya ta cira sama a baya-bayan nan, abin da masana ke alaƙantawa da ƙudurin gwamnatin ƙasar na fara aiwatar da tsarin bunƙasa tattalin arziƙi na taƙaitaccen wa’adi.
Wani dillali a kasuwar hannun jarin Nijeriya da ke Lagos, Dr. Ƙasimu Garba Kurfi ya ce darajar hannayen jarin manyan kamfanoni masu hulɗa da amfanin gona a kasuwar ta ɗaga sakamakon shirin bunƙasa noman rani da na damuna a ƙasar.
Hannayen jari a Nijeriya sun yi tashin da suka daɗe ba a ga irinta ba a daidai lokacin da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya koma gida bayan doguwar jinya a Ingila.
Ƙasimu Kurfi ya ce tashin darajar hannayen jarin ta faro ne bayan kamfanoni sun fara gabatar da bayanin hada-hadarsu a shekara ta 2016, wanda ya nuna cewa harkoki sun yi kyau, yayin da masu zuba jari suka samu riba.
Dillalin hannayen jarin ya ce matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka na sasantawa da matasan yankin Naija-Delta, ya yi tasiri wajen samun ingantuwar lantarki wadda ta taimaka wa kamfanoni rage kuɗaɗen da suke kashewa wajen sayen makamashi.
A cewarsa matakin ya nuna cewa alƙiblar Nijeriya ta fara ɗaukar kyakkyawan saiti.
Sai dai, ya ce ga alama har yanzu akwai jan aiki a gaban hukumomin ƙasar kan batun janyo hankalin masu sha’awar zuba jari, don kuwa rashin samun tsayayyen farashin dala tsakanin bankuna da kasuwar bayan fage ka iya rage musu karsashin zuwa Nijeriya.
Add Comment