Labarai

Ba Igbo Wa'adi: Kwararrun Majalisar Dinkin Duniya Sun Nemi A Hukunta Matasan Arewa

Wasu kwararrun Majalisar Dinkin Duniya kan hakkin dan Adam sun nemi gwamnatin tarayya kan ta hukunta matasan Arewan nan da suka ba ‘yan kabilar Igbo Wa’adi kan su fice daga yankin duk da yake sun janye wannan wa’adin a makon da ya gabata.
A wata sanarwar da kwararrun suka fitar sun yi nuni da wata waka da aka yi da harshen Hausa wanda aka ciki aka nemi Hausawa kan su lalata dukiya tare da kashe duk wani dan Kabilar Igbo da ya ki barin yankin idan wa’adin ya cika.
A cewar kwararrun irin wadannan kalamai na kiyayya na da matukar hadari ga zamantakewar al’ummar Nijeriya musamman idan aka yi la’akari da irin bala’in da yakin basasar kasar ya jefa mafi yawan al’ummar kasar. Don haka sun nemi gwamnati ta kara yin bincike tare d gurfanar da wadanda ke da hannu wajen bayar da wa’adin.