Labarai

Ba don kudi na koma PSG ba -Neymar

An samu bambancin ra’ayi daga manyan koci-koci dangane da farashin da PSG ta sayi Neymar

Dan kwallon Brazil Neymar ya ce “abin takaici ne mutane suyi tunanin cewa saboda kudi” ya koma Paris St-Germain.

Dan wasan mai shekara 25 ya koma kulob din Faransan ne a kan kudi sama da fam miliyan 200 ( Sama da naira biliyan 94).

 

A ranar Asabar ne Neymar zai buga wasa a PSG a karon farko cikin gasar Faransa da za a fara, sai dai ya ce kudinsa bai yi tsada ba.

Kocin PSG, Nasser Al Khelaifi, ya kara da cewa, Neymar zai iya samun karin kudi a wani kulob din.