Kannywood

Auren Sirri: Jarumar Kannywood Zahra Diamond Tayi Aure

Shahararriyar jarumar Kannywood Zahra Diamond tayi aure, a wata sanarwa da shafin kannywood Official suka fitar a safiyar yau da misalin karfe bakwai.

Ga abinda suka rubuta.

Muna farin cikin sanar daku cewa an daura auren Jaruma Zahra Muhammad wace akafi sani da (Zahra Diamond) muna addu’a Allah ya sanya Alkairee ya baku zaman lafiya

Sannan daga bisani sai mukaje ita shafinta na Instagram sai mukaga ta goge duk wani post da tayi sai guda daya mai dauke da sako kamar haka:

Sallam masoyana, producer dina, director da abokan aiki, wanda na gamawa aikinsu ina musu fatan alkairee, wanda bangamawa ba ina mai basu hakuri, sabo da yanayin zabin da Allah yakeyiwa dukkanin bayinsa, yayimin zabi mafi alkairee a gareni, sabo da haka bani da haki ko yancin karasa muku aikinku, fatan zaku fahimta, kuma Allah ya baku hakuri ya kuma musanya muku da mafi alkairee, dan Allah masu fans page dina kuyi hakuri ku duba girman Allah ku cire hotuna na da bidiyos dina, kuma ku canza sunan nagode.

Wannan shine sakon da muka samu a shafin nata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: