Ana ce-ce-ku-ce kan wasu hotuna da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Maryam Booth ta wallafa na bikin aure.
Jarumar ta wallafa hotunanta tare da Sadiq Zazzabi mawakin Hausa kamar ango da amarya, hotunan da ke nuna kauna da soyayya.
- Advertisement -
Hotunan sun ja hankalin mabiyanta da ma’abota fina-finan Hausa.
An ta yada hutunan a shafukan sada zumunta na intanet cewa Maryam Booth za ta yi aure.
Wasu na tunanin a fim ne, yayin da wasu ke cewa da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi ganin cewa mawaki ne da ba ya fitowa a fim.
BBC ta tuntubi Maryam Booth domin tabbatar da ko da gaske ne za ta auri Sadiq Zazzabi.
“Ban yi aure ba, a wani fim ne da ake kan shirya wa,” in ji ta.
Ta kara da cewa an dauki hotunan ne a wani fim mai suna Gidan Biki na hudu da suka fito tare da mawakin.