Daga Comr Abba Sani Pantami
Shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunne a kan auren mace fiye da daya wanda yayi ikirarin shine dalilin tabarbarewar ilimi a kasar nan.
A yayin magana a taron sarakunan jihar 17 da shugaban UBE na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a Gusau, Sarkin Anka wanda ya fara alakanta talauci da tara mata, yayi kira ga al’ummar Musulmi da su tabbatar da sun bai wa ‘ya’yansu ilimi na boko da zamani mai nagarta.
Basaraken ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ilimin zamani a jihar Zamfara da jama’arta baki daya.