Atiku Zai Yabawa Aya Zakin Ta Idan Ya Dawo -Lai Mohammed

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zargin badakalar milyan 159 : Atiku zai yabawa aya zakin ta idan ya dawo – Lai Mohammed

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai amsa wasu tambayoyi idan ya dawo daga kasar Amurka.

Talla

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana a cewa Atiku na da kashi a gindi cikin mutuwar bankin Bank PHB.

Lai ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai a fadar shugaban kasa a yau Juma’a.

Lai Mohammed ya kara da cewa dalilin da yasa gwamnatin zata tuhumi Atiku Abubakar shine wata sabuwar hujja da ta bayyana cewa ya amfani wasu makudan kudade wanda ya sabbaba mutuwar Bankin PHB.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Yace:”Wannan abu ya fara ne daga wata takarda da aka rubuta ranar 13 ga watan Junairu, 2009 na bukatar cire kudi milyan N159 domin Atiku,”

“Muna son ya gama zamansa a Amurka komin dadewa, amma wajibi ne yayi bayani ga yan Najeriya idan ya dawo.” inji Lai Muhaammed

Yayinda yake karin bayani kan ziyarar da Atiku ya kai Amurka, Alhaji Lai Mohammed yace gabanin yanzu, gwamnatin tarayya ta saki jawabi inda ta shawarci Amurka da kada ta bashi biza.

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: