Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri`u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ZABEN 2019

Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri’u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau

Talla

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya ce “babu tantama shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kan kujerarsa a zaben 2019 da izinin Allah.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

Mallam Shekarau ya ce zaben da za a yi a badi 2019 ba irin na 2015 bane. Musulmi da Musulmi ne kuma dan arewa ne da dan arewa a tsakanin APC da PDP. Don haka Buhari zai kada Atiku amma ba da irin rinjayen wancan yanayin ba.

Duka wadannan kalamai, Mallam Shekarau ya yi sune a ranar Talatar da ta gabata a garin Badun lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida, bayan an tashi daga taron kungiyar PSN wato masu harkar magani ta kasa inda suka karrama shi tare da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Ya kara da cewa wannan zaben karo da karo ne, amma Buhari ne mai nasara.

Ana sa rai za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 16 ga Fabrairu 2019, kuma ‘yan takara 74 ne za su shiga wannan zabe na shugaban kasa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: