Dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ya sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zabukan da za gudanar a shekara mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus ne ya bayyana haka a shafinsa na Tiwita.
Mista Secondus ya bayyana cewa ya jagoranci Atiku Abubakar zuwa cibiyar Bishop Kukah da ke Abuja inda ya sanya hannu a kan yarjejeniyar.
A jiya ne dai ‘yan takarar mukamin shugaban kasa a Najeriya suka rattaba hannu a kan takardar yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Amma Atiku Abubkar bai halarci taron ba duk da cewa tsohon shugaban Najeriya Abdussalam Abubakar wanda shi ne ke jagorantar wannan kokarin ya ce kwamitinsa ya gayyaci dukkan jam’iyyun siyasar kasar zuwa wajen wannan taron.