Atiku Abubakar Ya Ziyarci Ekweremadu
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP,Atiku Abubakar ya ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawa,Ike Ekweremadu.
A cewar wasu rahotanni Atiku ya ziyarci Ekweremadu domin su fahimci juna kan zabar Peter Obi da ya yi a matsayin mataimakinsa.
Tawagar mataimakin shugaban kasar ta ƙunshi, shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, shugaban jam’iyar PDP na kasa, Uche Secondus da kuma Austin Akobundu sakataren tsare-tsaren jam’iyar na kasa.
- Advertisement -
Zaben Peter Obi da Atiku yayi ya haifar da tada jijiyoyin wuya a yankin kudu maso gabas inda wasu masu ruwa da tsaki suka zargi Atiku da rashin tuntubarsu.
Gwamnan jihar Ebonyi,David Umahi a baya ya bayyana cewa jagororin PDP a yankin za su haɗu domin tattaunawa kan zabin na Obi amma daga baya ya janye maganar.
Duk da cewa mataimakin shugaban majalisar dattawan bai yi magana ba an rawaito cewa ya nuna rashin gamsuwarsa kan rashin saka sunansa a kunshin kwamitin jam’iyar na yakin neman zaben shugaban kasa.