ASUU: Babu Ranar Janye Yajin Aiki

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta ce ba za ta sauya ra’ayi ba kan yajin aikin da take yi wanda ya shafi daukacin jami’o’in gwamnati da ke fadin kasar.

Hakan ya zo ne duk kuwa da sake zaman tattaunawa da kungiyar ta yi tsakaninta da bangaren gwamnatin tarayya a ranar Litinin a Abuja.

Talla

Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige wanda ya jagoranci tattaunawar, ya yi wa shugabannin kungiyar alkawarin cewa gwamnati za ta bi duk matakan da suka dace domin biyan bukatunsu.

Bangarorin biyu sun amince su sake haduwa domin ci gaba da tattaunawa a ranar Litinin 10 ga watan Disamban 2019.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Shugaban kungiyar Farfesa Ogunyemi ya ce za su dakata har zuwa rana ta gaba da za a sake zama tsakanin kungiyar da gwamnati domin yanke hukunci kan ko za su janye yajin aikin ko kuma za su ci gaba.

Ya ce hakan zai ba su damar lura da irin matakan da gwamnatin tarayya za ta dauka wajen cika alkawurran da ta dauka na biyan bukatunsu.

Gwamnati da kungiyar sun sha zama sau da dama, domin tattauna yadda za a kawo karshen yajin aikin.

ASUU ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 4 Nuwamba, domin nuna rashin dadi game da karancin kudi da gwamnati ke bai wa jami’o’i, da zargin cewa ana shirin karin kudin makarantar dalibai da kuma rashin aiwatar da yarjeniyoyin da kungiyar ta cimma da gwamnatoci a baya.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: