Asiri Aka Yi Wa Buhari, Cewar Honarabul Gudaji Kazaure

21

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Asiri Aka Yi Wa Buhari, Cewar Honarabul Gudaji Kazaure

…ina kira ga ‘yan Shi’a su daina yi wa Buhari Alkunut

Daga Aminu Baka Noma Sani Mainagge

Dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Honarabul Gudaji Kazaure ya bayyana cewa asiri aka yi wa shugaba Muhammadu Buhari shi ya sa har yanzu bai dawo gida ba daga jinyar da yake a kasar Burtaniya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 906

Dan majalisar ya kara da cewa asiri ne ya hana shugaban cin abinci amma dai yana samun sauki.

 

Honarabul Gudaji ya yi wannan furuci ne yayin wata hirar kai tsaye da ya yi da gidan rediyon Dala FM dake jihar Kano.

Honarabul Gudaji Kazaure ya kuma shawarci mabiya darikar shi’a da su daina yi wa shugaban kasa Alkunuti domin abinda suke zarginsa da shi ba laifinsa bane. Tsokanar da suka yi wa sojoji ce ta jawo musu duk abinda aka yi musu.

Ya kuma bayyana cewar gaskiya ne an saya musu motoci kirar fijo, amma kudinta a kasuwa bai wuce naira milyan 13 ba.

Copy From Rariya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.