Raayi

Ashe Sune Sanadin Hada Bangarorin Boko Haram Yaki Da Juna

Jama’a ku nutsu ku karanta wannan bayanan da kyau
Tsarki ya tabbata ga Allah, rikicin bangarorin kungiyar Boko Haram abin boye ya fara fitowa fili, marigayi shugaban sojoji Janar Ibrahim Attahiru da shugaban leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro na rundinar sojin Nigeria marigayi Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune sanadin haddasa tsoho da sabon rikici tsakanin ‘yan Boko Haram wanda ake kyautata tsammanin Shekau ya yi mushe.

A cikin wani sabon rahoto wanda jaridar PR Nigeria ta wallafa jaridar da take da kusanci da rundinar sojin Nigeria, tace marigayi Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya shine yake jagorantar tawagar mayaka sojojin kundunbala a lokacin da marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yake matsayin babban kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole a Arewa maso gabashin Nijeriya.

Kafin a cire shi, a lokacin wasu tawagar mayakan Boko Haram sun tuba sun mika kai wato sun yanke shawaran ajiye makamansa wa rundinar Operation Lafiya Dole, to sai marigayi Birgediya Janar Abdulrrahman Kuliya ya bada shawara wa babban kwamandan rundinar marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru shawaran cewa a bar tubabbun mayakan na Boko Haram cikin sansanin Boko Haram, domin su zama masu leken asiri wa sojoji, sannan ayi amfani dasu wajen haddasa sabani a tsakanin Boko Haram.

Yana daga cikin dabarun yaki a ilmin tsaro, idan akwai kungiyoyi cikin ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga, to idan har gwamnati ko hukumomin tsaro tana so ta karya su, to sai tabi wasu hanyoyin sirri ta haddasa rikici da sabani a tsakanin kungiyoyin, hakan zai zama sanadi na tarwatsewar su

To a lokacin Janar Attahiru ya amince da shawaran na Janar Kuliya, wanda hakan ya taimaka sosai wajen gwara kawunan bangarori biyu na Boko Haram, wato bangaren ISWAP na su Habib Muhammad Yusuf Al-barnawiy da Boko Haram na Abubakar Shekau.

Bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya nada marigayi Janar Attahiru a matsayin sabon shugaban sojojin kasa na Nigeria wanda ya maye gurbin Janar Buratai, sai Janar Attahiru ya dauko Janar Abdurrahman Kuliya ya bashi jagorancin bangaren Intelligence na rundinar sojin Nigeria domin su daura daga inda suka tsaya lokacin da suke jan ragamar rundinar Operation Lafiya Dole suka gwara kan ‘yan Boko Haram.

Bai wuce sati biyu ba, rundinar sojin Nigeria karkashin jagorancin Janar Attahiru ta canza sunan rundinar da take jan ragamar yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas daga OPERATION LAFIYA DOLE zuwa OPERATION HADIN KAI da manufar samar da cikakken hadin kai tsakanin tubabbun ‘yan Boko Haram da sojojin kundunbala, marigayi Janar Abdulrahman Kuliya na daga cikin wadanda suka bada shawaran canzawa rundinar suna.

Hakan yayi tasiri matuka a jejin sambisa, tun daga rikicin raba man fetur da ya faru a tsakanin ‘yan Boko Haram bangaren Shekau da Al-barnawiy akan iyakar Kamaru da Nigeria suka gwabza yaki da juna, da rikicin da ya haddasa Shekau ya kashe wasu Kwamandojin yakinsa guda hudu wanda ya zarga da kokarin cin amanarsa wajen sanar da bangaren su Al-barnawiy maboyarsa na sirri dake kan tsaunin dutsen mandara a yankin Gwoza.

Wanda hakan ne ya taimaka wa su Al-barnawiy suka gano inda Shekau yake zuwa ya wuni suka rutsashi a can, a zaman sulhu akace Shekau ya tarwatsa kansa da bomb ya hallaka da wadanda ake zaman da su, kwana daya da ya fitar da audio wanda zakuji yana fadin sakon cewa anci amanarsa duk da ya kashe wadannan kwamandoji guda hudu nasa, amma su Al-barnawiy sun isa yadda yake, abinda ake tunanin yanzu haka Shekau yayi mushe duk da dai har yanzu babu tabbaci.

Marigayi Janar Ibrahim Attahiru da Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune sanadin haddasa wannan mummunan rikici tsakanin ‘yan Boko Haram a jejin Sambisa wanda ake tunanin Shekau yayi mushe ya zama abincin wutar jahannama, shin maciya amanar tsaron Nigeria zasu barsu su wanye lafiya saboda suna ganin wadannan jarumai da gaske suke zasu kawar da Boko Haram?

Me yasa suka fado a jirgi lokaci daya suka mutu?, anya kuwa..?

Sai na yanzu nake tuna abinda ya faru lokacin da shugaba Buhari ya cire su Buratai ya kawo su Attairu, babu wanda aka biya jaridu kudi aka masa batanci kamar Janar Attahiru, tun daga hawansa, bai ma shiga ofis ba aka fara masa batanci, a Nigeria ba’a biyan kudi a jaridu a bata mutanen banza maciya amana, mutanen kirki ake batawa, jama’a ku tuna wannan.

Insha Allahu Nijeriya sai ta ga bayan Boko Haram ko da maciya amana ba su so hakan ba.

Allah Ka karbi shahadar su Janar Attahiru
Allah Ka maye mana gurbinsu da wadanda zasu zama sanadin kawar da Boko Haram daga doro duniya Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Daga Datti Assalafiy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: