Komawar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kasar ranar Asabar bagatatan ta sanya murna sosai a zukatan masoyansa a fadin kasar.
Shugaban, wanda ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a Landan, ya samu tarbar Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministoci da jami’an tsaro da sauran jiga-jigan gwamnatinsa.
A yayin da wasu ke murnar komawarsa gida, su kuwa masu fafutikar ganin Shugaba Buhari ya koma kasar ko kuma ya sauka daga mulki sun ce matsin lambarsu ce ta tilasta masa komawa gida ba tare da shiri ba.
A daren Juma’a ne dai wasu masu fafutikar suka isa kofar gidan da shugaban ke jinya a Landan inda suka yi ta ife-ife da kira a gare shi ya koma Najeriya ko kuma ya ajiye mukaminsa.
Daya daga cikinsu Deji Adeyanju, ya wallafa a shafinsu na Twitter cewa masu fafutikar sun kwana a kofar gidan suna kira ga Shugaba Buhari ya samawa kansa lafiya ya koma Najeriya ko ya sauka daga mulki.
A cewarsa, har sai da ta kai wani jami’i da ke cikin gidan ya fito ya ba su hakuri su daina ihu saboda shugaban na son yin bacci.
Sai dai a hirar da ya yi da manema labarai a Abuja bayan komawar shugaban kasar gida, Mai magana da yawunsa Femi Adesina ya musanta ikirarin masu fafutikar.
Ya kara da cewa likitocin Shugaba Buhari ne suka sallame shi bayan sun tabbatar da samun saukinsa.
Gabanin komawar shugaban kasar Najeriya dai, masu fafutikar, karkashin jagorancin Charles Chukudifu Oputa wanda ake yi wa lakabi da Charly Boy sun kwashe makon jiya suna gangami a Abuja, babban birnin kasar domin matsa lamba a kansa ya koma gida.
A daya daga cikin gangamin, wanda Charly Boy ya yi a kasuwar Wuse da ke Abuja, sai da aka samu hatsaniya lamarin da ya tilasta masa tserewa domin kada a illata shi.
Sai dai wasu mutane da ake zargi magoya bayan shugaban kasar ne sun yi kaca-kaca da motarsa.
Su dai masu hoto bayan Shugaba Buhari sun yi zargin cewa an dauki hayar masu fafutikar ne domin cin mutuncin shugaban.
Sun kara da cewa bai kamata a tilasta masa komawa kasar ba saboda sai da ya mikawa mataimakinsa ragamar tafiyar da Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukaci Shugaba ya yi duk lokacin da zai fice daga kasar.
Da alama dai komawar da Shugaba Buhari ya yi Najeriya za ta bude sabon babi na tafiyar da harkokin kasar saboda sauye-sauyen da ake sa ran zai yi a harkokin mulki ta yadda za a samu ci gaba musamman a fannin tsaro da tattalin arziki da yaki da cin hanci, wadanda su ne ginshikin yakin neman zabensa.
Source BBC hausa
Add Comment