Kannywood

Asase ya ƙaryata masu cewa gwamnati ta dakatar da nuna shirin ‘A Duniya’

FURODUSA kuma jarumi Tijjani Abdullahi (Asase) ya ƙaryata raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa wai gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da nuna shirin sa na ‘A Duniya’ a YouTube.

Ji-ta-ji-tar ta bazu ne bayan da mujallar Fim ta wallafa wani labari a ranar Laraba da ta gabata kan yadda gwamnatin jihar ta bayyana wani ƙudiri na kawo gyara a kan yadda ake haska fim ɗin wanda kamfanin Brainscope na Asase ke nunawa.

A labarin, mun ruwaito cewa mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin makarantun tsangaya, Sharif Ahmadu Shu’aibu, ya fitar da wata takarda inda ya ce zai kawo gyara a kan yadda ake haska fim ɗin sakamakon ƙorafin da wasu masu kallo su ka gabatar mata. Amma ofishin bai bayyana ko su wanene ba.

A cikin wani faifan bidiyo na tsawon minti 1 da ya wallafa a Instagram, Asase ya ce shi har yanzu ya na nan ya na haska fim ɗin shi.

Ya ce, “Kamar yadda ji-ta-ji-ta ta ke yaɗuwa yanzu a soshiyal midiya kan cewa an dakatar da shirin fim ɗin ‘A Duniya’, to gaskiya ba haka ba ne, gwamnati ba ta dakatar da shirin fim ɗin ‘A Duniya’ ba.

“Kamar yadda kowa ya sani, ana ci gaba da haska fim ɗin a tashar mu ta Zinariya Hausa da ke kan YouTube. Ba a dakatar da shi ba. Kuma mu na nan mun ci gaba da yin aikin mu ana kawo ba.”

Jarumin ya alaƙanta wannan batu da cewa, “Hassada ce kawai ta mutane, shi ya sa su ke wannan rubuce-rubuce a kan cewar ba su da buƙatar fim ɗin.”

Asase ya ce akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin sa da gwamnati, kuma shi da sauran masu shirya fim ɗin su na bin doka sau da ƙafa.

Ya ce: “Duk wata doka da ƙa’ida da ake bi ta gwamnati ba wacce ba mu bi ba, kuma mu na bin doka, kuma mu mu na masu biyayya ga gwamnatin Jihar Kano da duk abin da ta zo da shi, kuma mun yarda za mu bi doka, za mu bi tsari.”

Jarumin ya jaddada cewa, “Duk abin da ya saɓa wa addinin mu ko ya saɓa wa al’adar mu mu na ƙoƙarin yadda za mu kauce mishi don mu zauna lafiya.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: