Labarai

Asarar Naira Milyan 160 Aka Tafka A Gobarar Majalisar Dokokin Jihar Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Kwamitin da majalisar dokokin jihar Katsina ta kafa domin gano musababbin tashin gobarar da kuma tantance yawan asarar da aka yi, karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar kuma dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rimi, Honarabul Abubakar Korau Abukur ya bayyana cewa an yi asarar miliyan dari da sittin.

Honarabul Abubakar Korau ya bayyana haka ne a lokacin da kwamitin ke mika rahotansa gaban Shugaban Majalisar Jihar Katsina a jiya Laraba.

Korau ya kara da cewa musababbin tashin gobarar ya samo ne daga wutar lantarki a cikin dare kuma majalisar ba ta da karaurawar nan, wadda idan gobara ta tashi, za ta dunga yin kuwwa.

Shima da yake jawabi, Shugaban majalisar dokokin jihar Katsina, Honarabul Tasi’u Musa Maigari ya yaba wa membobin na yadda suka gudanar da aikin cikin lokaci, kuma majalisar za ta yi amfani da duk shawarwarin da kwamitin ya bayar domin aiwatarwa domin kaucewa afkuwar makamanciyarta anan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: