Labarai

Anya za a iya daina shigowa da shinkafa Nigeria?

Jihar Ebonyi na kan gaba wurin samar da shinkafa a Najeriya
Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta sha alwashin daina shigowa da shinkafa cikin kasar daga shekarar 2018, saboda ta gida za ta wadata.
Gwamnatoci a matakai daban-daban na ci gaba da fadi tashin nemo hanyoyin fitar da kasar daga halin karayar arziki mafi muni da ta fada a bara.
Daya daga cikin wadannan matakan shi ne mayar da hankali ga aikin noma na duke tsohon ciniki.
Hukumomin kasar dai, sun dukufa ne ga noman shinkafa domin wadatar da kasar da abinci da kuma samun kudaden shiga da ba su da alaka da danyen mai.
Irin wannan yunkuri na baya-bayan nan shi ne kaddamar da shirin noman rani na shinkafa da gwamnatin jihar Zamfara ta yi a garin Gumi.
Gwamnan jihar Alhaji Abdul-Aziz Yari Abubakar, wanda ya kaddamar da shirin, ya ce zuwabadi babu maganar shigowa da shinkafa kasar kamar yadda suka yi alkawari ga jama’a.
A matakin farko na wannan shiri, manoma 2150 ne aka baiwa tallafin kudi da iri da taki da kayan noma.
Sai dai wasu na ganin zai yi wuwa a iya daina shigowa da shinkafar waje Najeriyar saboda rashin ingancin ta gida.
Kuma duk da nasarar da ake cewa an samu wurin bunkasa noma a ‘yan watannin da suka wuce, har yanzu farashin abinci bai sakko ba a kasar.