Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da bular wata cutar dabobi mai yaduwa da ake tsamanin cutar huhu ce da ke kashe shanu a jihar.
Jami’in yada labarai da hulda da Jama’a na ma’aikata r Noma da Gandun Daji na jihar Dahiru Abdullahi ya sanar da bullar cutar a wata zantawa ta wayar tarho da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Abdullahi ya ce, an samu bullar wata cuta da ba a gano kanta ba a wasu sassan jihar, wanda kawo yanzu likitocin dabobi sun fara daukar jinin dabobin da suka mutu domin yin gwaji a dakin bincike saboda a gano wane irin cuta ce.
Kamfanin dillancin labaran NAN ya ruwaito cewa, an samu bullar cutar ne a wasu garuruwan kananan hukumomin Kachia da Kagarko da kuma Anchau.
- Advertisement -
Wani bafulani da ke kiwo mai suna Suleiman Adamu ya shaidawa manema labarai cewa, a halin yanzu cutar da kashe fiye da shanu 100 a garken su da ke mazabar Doka a karamar hukumar Kachia a cikin makonni uku.
Adamu ya ce, mahaifin su Alhaji Dano da ke da shanu fiye da 500 yana cikin fargabar da tsoro sakamakon bullar wannan cuta da ke kashe dabbobi ba kakkautawa.
NAN ta ruwaito cewa, shanun da suka kamu da cutar ba su iya numfashi cikin sauki, wadda hakan babban matsala ce a gare su, sauran alamomin cutar sun hada da tari musamman idan daba ta yi tafiya ko gudu.
#Mikiya