Addini

Annabi Ya Yi Tasbihi Ne Da Yatsun Hannunsa – Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo

Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi tasbihi ne da yatsunsa na dama, haka nan ya yi umurni da a yi tasbihi da yatsu. Babu ingantaccen Hadithi game da yin Tasbihi da wanin yatsu. Lalle dukkan shiriya na cikin abin da ya tabbata daga shi Annabi mai tsira da amincin Allah cewa: Ya ce a yi, ko ya aikata, ko aka aikata a gabansa bai hana ba.
  1. Ibnu Hibban ya ruwaito Hadithi na 843, da Abu Dawuda Hadithi na 1503, da Tirmiziy Hadithi na
3740, da Nasa’iy Hadithi na 1280, da Hakim Hadithi na 2005, da Tabraaniy cikin Mu’ujamul Kabir Hadithi na 1482, da Bazzar Hadithi na 2406 da isnadi sahihi daga Abdullahi Bin Amr ya ce: (( ﺭﺃﻳﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﻌﻘﺪ ﺍﻟﺘﺴﺒﻴﺢ ﺑﻴﻤﻴﻨﻪ )) Ma’ana: ((Na ga Annabi mai tsira da amincin Allah yana kulla Tasbihi da damansa)).
  1. Abu Dawud ya ruwaito Hadithi na 1501, da Tirmiziy Hadithi na 3823, da Ahmad Hadithi na 27134, da Tabraaniy cikin Mu’ujamul Kabir Hadithi na 20692 da isnadi sahihi daga Sahabiya Yusairah ta ce:
(( ﺍﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻣﺮﻫﻦ ﺍﻥ ﻳﺮﺍﻋﻴﻦ ﺑﺎﻟﺘﻜﺒﻴﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﺪﻳﺲ ﻭﺍﻟﺘﻬﻠﻴﻞ ﻭﺍﻥ ﻳﻌﻘﺪﻥ ﺑﺎﻻﻧﺎﻣﻞ ﻓﺈﻧﻬﻦ ﻣﺴﺆﻭﻻﺕ ﻣﺴﺘﻨﻄﻘﺎﺕ ))
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya umurce su su mata da su maida hankali a kan yin Takbiri, da Taqdisi, da Tahlili, kuma su kulla tasbihin da yatsunsu saboda lalle su yatsun abubuwa ne da ake tambaya ake kuma sanya su su yi magana)).
Allah Ya taimakemu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.