Labarai Siyasa

Ankori Abdullahi Abbas Daga Shugabancin Jam’iyyar APC a Kano

Rikici ya ɓarke a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano domin kuwa tsagin jam’iyyar da Hussaini Isa Mairiga ke shugabanta ya dakatar da Abdullahi Abbas daga shugabancin jam’iyyar.

Da ma dai tsagin jam’iyyar ta APC a Kano wanda ya ƙunshi ‘yan rusassun jam’iyyun ANPP, CPC da ANC ya daɗe yana ƙorafi a kan shugabancin Mista Abbas, kuma tsagin ya zargi Mista Abbas da wuce gona da iri a jam’iyyar.

‘Yan waɗannan rusassun jam’iyyun sun yi zargin cewa tun farko ma, zaɓen da ya ba Abdullahi Abbas nasarar zama Shugaban Jam’iyyar APC na Kano ba ya bisa ƙa’ida, kuma ya saɓa da kundin tsarin mulki.

“Kodayake, Abdullahi Abbas ya zama Shugaban Jam’iyyar ne ta hanyar zaɓen bogi, maimakon ya sasanta da kowa sai yake ta yin shugabanci da ɗagawa”, in ji Mista Mairiga.

Mista Mairiga ya yi gargaɗin cewa: “Gaskiyar ita ce shugabancinsa ya saɓa wa kundin tsarin mulki kuma ba ya bisa doka, duk wani abu da ya zo a ƙarƙashin su ɓatacce ne.

“Ina nufin, duk wanda ya yi takara a zaɓen ƙananan hukumomi na Janairu, 2021 a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas yana ɓata lokacinsa ne saboda ko ya ci zaɓe a banza.

“Za ku iya ganin hanyar da aka bi don fitar da ‘yan takara a zaɓen ƙananan hukumomin a cike take da maguɗi kuma ba a yi dimokuraɗiyyar ba, an ƙi siyar wa kowa fom sai na kusa da su.

“Wannan ita ce ɗagawa da mutum zai iya gani a tsarin dimokuraɗiyya kamar wannan da muke yi, shi yasa gaba ɗaya muka yadda mu cire shi daga shugabancin jam’iyyar, kuma duk wani abu da ya zo daga ƙarƙashin sa ɓatacce ne”, Mista Mairiga ya ƙara da haka.

Ya yi kira ga hedikwatar APC ta ƙasa da ta aiko da shugabancin riƙo wanda zai sa a yi sabon zaɓen a jam’iyyar APC a Kano don samun ci gaba, yana mai gargaɗin cewa gaza yin haka zai sa APC ta yi faɗuwar baƙar tasa a jihar Kano.

Madogara

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement