Ankaiwa Sani Wawo Mummunan Farmaki

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sani Wawo matashi ne da kwanan nan ya shahara wajen wakar sa da yake ta ban dariya har takai ana gayyatar sa zuwa majalisi yana cashiya har ma yana samun abin hannu,kuma sannu a hankali kasuwar ta bude har ya sayi mota.

Amma kwanaki biyu da suka gabata wani matashi mai suna Yusif Dan mai unguwa ya sossoka masa wuka bisa yunkurin hallaka shi,koda yake babu cikakakken bayani akan dalilin kaiwa Wawo mai wakar Malam buda mana littafi wannan hari amma da yawa wasu na ganin cewar farmakin baya rasa nasaba da yadda ya fara samun abin hannu.

Amma yau mun yi magana da shi Wawo mai wakar “kowanne tsuntsu kukan gidan su yake” wanda ya bayyana min cewar yayi mamakin yadda aka bayar da belin wanda yayi masa wannan aika aika,kuma a lokacin da muke magana dashi yake shaida min cewar mahaifin yaron ya debo tawaga zuwa gidan su domin bayar da hakuri.Amma yace fargabar sa ita ce,shi dai bashi da gata, amma bai san dalilin bayar da belin wanda yayi yunkurin kashe shi ba.

Koda yake mawakin barkwancin yana nan da ransa amma har yanzu idan yayi kaki jini ne ke fita.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 662

Muna rokon Mahukunta su binciki wannan magana domin tabbatar da adalci tsakanin Dan talaka da Dan Mai Unguwa.Allah ya kiyashe mu ya shirya mana zuri’a

Sani wawo

#Nasir Zango

 

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: