Gwamnatin jihar Kano ta bawa makarantun jinya (College of Nursing) dana ungozoma (College of Basic Widwife) damar fara siyarda form na daukar sababbun dalibai.
Ga matakai daki daki akan yadda wanda keson shiga makarantun zebi
Mataki na Farko (1) : Ziyarci https://moh.knstate.healthcare
Mataki na Biyu (2): Se ku danna Apply ko Start Application.
Mataki na Uku (3): Seku saka Email address wanda yake aiki sanna ku danna Submit.
Mataki na Hudu (4): Se kuje email dinku ku duba Inbox ko kuma spam folder zakuga sako seku danna link din dake cikinshi domin tabbatar da email dinda kukai rijista dashi ma’ana kuyi verify na email dinku.
Mataki na Biyar (5): Seku cike wadannan bayanan
- First name
- Last name
- Phone Number
- Makarantar da kake
- Abinda kakeson karantawa (Course)
- Sekuma password
Mataki na Shida(6) Kuyi Download din invoice na biyan kudi wanda suka samar bayan gama rijista se kubi matakan dake cikinshi (instructions).
Mataki na Bakwai (7): KU garzaya Bankin Sterling Bank dake kusa daku domin biyan kudin dake cikin invoice wace kukai generating.
Mataki na Takwas (8): Ku garzaya Makarantar jinya ko ungozoma (College of Nursing and Basic Widwifery) shashen bursery (Bursery Unit) da takardar shedar biyan kudi da kukayi a banki domin tantancewa.
Mataki na Tara (9): Seku ziyarci https://moh.knstate.healthcare/login
Mataki na Goma (10) : Seku saka Email da password da kukayi rigista domin kammala rigistration.
Mataki na Sha Daya (11): Se kubi matakan da suke a Student’s Dashboard.
Mataki na Sha Biyu (12): Se kuyi firintin (Print) Acknowledgement Slip yayin da kuke jiran lokacin da za ai jarabawa(Time), ranar da za ai jarabawa(Date) da kuma gurin da za ai jarabawa (location) a applicant dashboard ko kuma email address.
Domin karin bayani ku tuntubesu a [email protected]
Add Comment