Labarai

Ana zargin shugabannin wata hukuma a Neja da yiwa Biliyan N1.2 kashe mu raba

Ana zargin shugabannin wata hukuma a Neja da yiwa Biliyan N1.2 kashe mu raba

DAGA HAUSA TIMES: Ana zargin ofishin cimma muradin karni na jihar Neja da yin sama da fadi da zunzurutun kudi har Naira Biliyan 1.2 na kudaden da aka ware domin yiwa talakawa aiki a jihar.

Majiya mai tushe ta ruwaito shuwagabannin hukumar sun rika rubuta ayyukan bogi tare da kara yawan ayyukan da sukace sunyi kamar sayowa da raba motocin daukar mararsa lafiya da injin janaraito a asibitocin jihar wanda kuma bincike ya nuna karya ne.

 

Kazalika suna rubuta sun bayar da kwangilolin na miliyoyin kudade har ma su rubuta sun bayar da kashi 30 na kudaden ayyukan wanda wannan ma duk bincike ya nuna karya ne.

Northern City News ta ruwaito jami’an hukumar cimma muradin karnin (SDG) sun rubuta sun kama hayar gida mai daki Biyu ga yan bautar kasa dake aiki tare dasu akan kudi miliyan N1.5 sabanin N150,000 wanda shine hakikanin kudin da suka biya na kama hayar.

Hausa times ta ruwaito wani ne ya ya tsegumtawa Gwaman jihar Nejan, Abubakar Bello badakalar da ake tafakawa a hukumar.

Bayanai sunce samun rahoton keda wuya sai Gwamnan ya sanya kwamishinan yan sandan jihar ya binciki badakalar a yayinda ya dakatar da wasu daga cikin wadanda ake zargin har a kammala bincike.

Sai dai jaridar Punch ta wallafa a shafinta cewa an zargi Gwamnan da cewa bai sauke wani daga cikin wadanda ake zargin ba wanda hakan ka iya kawo tarnaki a binciken.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Neja, Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis yace yanzu haka an fara kamo wasu da keda hannu a badakalar.

Yace kwamishinan yan sandan zai gabatarwa da Gwamnan sakamakob binciken da zaran sun kammala.

Jama’a kun dai ji shin ya kuke kallon wannan lamari?

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.