Wasanni

Ana Zargin Dan Wasan Premier League Da Lalata Da Kananan Yara

Ana zargin wani dan wasan dake buga gasar firimiyar Ingila da yin lalata da kana nan yara sai dai ba’a fadi sunan dan kwallon ba mai shekara 31 saboda matakan shari’a, wanda ke tsare a hannun ‘yan sandan Greater Manchester.

Kungiyar da dan kwallon ke yi wa wasa ta sanar cewar ta dakatar da shi ta kuma ce za ta ci gaba da bai wa mahukunta hadin kai kan binciken da ake yi, daga nan ta ce ba za ta kara cewa komai ba.

Sai dai tuni aka bayar da belin dan wasan, sannan ana kan ci gaba da bincike, kafin daukar mataki na gaba kuma hakan na zuwa ne yayinda cikin watan Agusta aka tsara za’a fara kakar Premier League ta bana wato ta shekarar 2021 zuwa 2022.