Kannywood

Ana Wata Ga Wata: An Samu Wani Jarumi Mai Kama Da Ibro

A yayin da masoya, yan uwa da kuma masu sha’awar kallon fina-finan Hausa ke ta jimami na rashin fitaccen jarumin nan na barkwanci watau Rabilu Musa IBRO, kwatsam sai ga wani mai kama da shi ya bayyana a masana’antar ta kannywood.

Matashin dai mai suna Alasan Kanu mazaunin Hotoro ne dake a jihar Kano a arewacin Najeriya ya fara fitowa fina-finai ne kwanannan inda kuma ya ke kwatanta barkwanci a ciki tamkar dai marigayin jarumin Rabilu Musa.

An samu labarin cewa yanzu haka dai matashin sabon jarumin Alasan Kanu ya samu damar fitowa a wani sabon fim mai suna ‘Jiki Magayi‘ wanda a ciki kuma ya taka muhimmiyar rawa.

Idan ba’a manta ba dai Allah ya karbi ran marigayi Rabilu Musa Ibro ne kimanin fiye da shekara daya kenan bayan ya sha fama da gajeruwar rashin lafiya inda kuma har yanzu ba’samu wanda ya cike gibin sa ba.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.