Addini

ANA WATA GA WATA: Duk Wanda Ya Yi Sallah Gobe Laraba Zai Yi Azumi 61, Cewar Sheikh Abbas Jega

Daga Tukur Sani Kwasara
“Duk wanda ya yarda ya rutsa ya ci abinci gobe ya ki bin umurni mahukunta lallai hakika zai ranka azumi 61. Ko ka ranka a nan duniya ko ka hadu da azabar Allah ta nan duniya da Lahira.

Kada ku bi kowane Malami ya ba ku umarni cewa ku ajiye azumi wai an ga wata.

Ku yi hattara da sabawa Allah, hukuncin Allah ta kowane gefe yana iya kama ka.

Ya Jama’a wanda ya yi Azumi 29 guda daya ke zama jidali..

Jama’a Musulmi ku ji tsoron Allah kuma kowa ya tsaya matsayar sa.

Allah Ka kare mu da bin son ranmu”, cewar Sheik Abbas Jega.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: