-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Ana Tilastawa Ma’aikata Shan Fitsari Da Cin Kyankyasai?


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Duk ma’aikacin da ya gaza, sai ya cika cikinsa da wannan

An daure wasu manajojin wani kamfani a China domin sun tilastawa wasu ma’aikatansu shan fitsari da cin kyankyasai.

‘Yan sanda sun dauki mataki bayan da wani bidiyo ya bayyana inda ake nuna ana dukan wasu ma’aikata da bel, kana suna shan wani abu mai launin ruwan kwai.

An kuma wallafa wasu labarai a shafukan sada zumunta da ke cewa an rika sa ma’aikatan su ci kyankyasai idan suka gaza cimma bukatar da kamfanin ya dora masu.

An daure manajoji uku na tsawon kwanaki biyar zuwa 10 saboda wannan laifin, kamar yadda jaridar South China Morning Post ta ruwaito.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Wani bidiyon da aka wallafa a shafin sada zumunta na China, Weibo, ya nuna lokacin da ake dukan wani ma’aikaci da bel bayan an tilasta masa tsaya a tsakiyar kawanyar abokan aikinsa.

An nuna wasu ma’aikatan kuma na shan wani abu mai launin ruwan kwai a kamfanin gyaran gida da ke birnin Guizhou, kuma sun rika toshe hancinsu a yayin da suke shan abin.

An kuma nuna hotunan wasu sakonni da aka ce manajojin kamfanin ne suka rubuta, wadanda aciki suke gargadin ma’aikatansu cewa za su ci kyankyasai idan ba su kara kwazo ba.

Kamar yadda wasu arahotanni suka bayyana, an rika horas da ma’aikatan ta hanyoyi daban-daban, kamar sanya su su sha ruwan masai, ko aske masu gashin kansu gaba daya.

An kuma ce kamfanin ya kasa biyan ma’aikatansa albashinsu na wata biyu kuma ma’aikatan na tsoron kwarmata batun domin za su rasa kudaden idan suka ajiye aiki.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: