Labarai

Ana Kokarin Dawo Da Buhari Nijeriya Kafin A Rufe Filin Jirgin Sama Na Abuja

Jaridar Sahara Reports ta rawaito a shafinta cewa hadiman shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari sun mayar da hankali wajen yi duk mai yiwuwa wajen dawo da shugaban gida Nijeriya kafin ranar da za rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Abuja
Tuni dai gwamnatin tarayya ta bayar da damar a rufe filin jirgin saman na Abuja na tsawon makonni 8 daga ranar Talata mai zuwa, 7 ga watan Maris
A cewar majiyar tamu ta Sahara Reports: “Wasu daga cikin makusantan shugaba Buhari na kokarin yin duk mai yiwuwa wajen dawo da shugaban gida Nijeriya tun kafi ya kammala wa’adin da aka deba masa na jinya a kasar Ingila, kafin a rufe filin jirgin sama na Abuja na tsawon makonni 8”
Majiyar Sahara Reporters ya ci gaba da cewa “Wadanda dai suka hana a fada wa’yan Nijeriya ainahin rashin lafiyar da ke damun shugaba Buhari wa ‘yan Nijeriya sune suke kokarin su dawo da shi bakin aiki kafin ya kammala jinya”
“Wadannan makusanta shugaba Buhari na can cikin gida na karkashin jagorancin Mamman Daura da hadiminsa Tunde Sabiu”, inji majiyar

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.