-Advertisement-


Ana Kan Farautar Wadanda Suka Yada Bidiyon Tsiraicin Maryam Booth


1 1,273

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An soma farutar mutane biyu da a ke zarginsu da dauka da kuma yada bidiyon tsiraicin jarumar fim din Kannywood mai suna Maryam Booth.

Hoton bidiyon wanda a ke zaton ya shafe tsawon shekaru uku da dauka ya zamo abun cece kuce a dandalin soshiyal midiya. Tuni dai shugabannin masana’antar Kannywood suka bai wa jami’an tsaro hadin gwiwa wajen kama wasu mutane biyu da a ke zargin su da daukar hoton bidiyon na Maryam Booth tsirara tare yada shi yanar gizo.

Jiya ne dai wani bidiyo wanda bai hauwa tsawon sakanni uku ba wanda ya bulla a shafukan sada zumunta da kafafen sadarwa. kuma yanzu haka hoton ya bazu a kan yanar gizo. Abun da ya ja maganganu a kan sa ya zamo mafi yawa a dandalin Twitter a tsakanin yammacin jiya da yau.

Kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito cewa an dauki wannan bidiyo kimanin shekaru uku da suka gabata. Kuma bidiyon na dauke ne da jarumar tsirara haihuwar uwarta, kamar dai ta fito daga wanka ta na kokarin sanya dan kamfanta, sai a ka dauki bidiyon.

Tuni shugaban kungiyar Kannywood na jihar Kano, Alhassan Kwalle, ya bayyana a majiyar ta mu cewa, kungiyar ta shiga cikin wannan lamari, kuma za ta taimaka wajen kamo mutane biyu namiji da mace da a ke zargin su da daukar hoton da kuma yada shi, bayan sun jima suna karbar kudi a wajen ta tare da yi mata barazana ga rayuwar ta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

-Advertisement-

Ya ce, “Gaskiya wannan abu ne da ya shafi rayuwar ta, ba harkar fim ba ce. Amma abun da muka gano shi ne wannan bidiyon an dauke shi kusan shekaru uku da suka shude. Kuma wadanda suka yi wannan abu suna yi mata barazana da shi, akan ta ba su kudi, idan kuma ba haka ba za su yada bidiyon duniya ta gani, hakan ya sanya take ta basu kudi duk lokacin da suka bukata”.

Ya kara da cewa “A ranar Larabar nan ne da ta gabata daya daga cikin su ya bukaci ta ba shi kudi zai kai mahaifiyar sa asibiti, ita kuma ta ce ba ta da kudi sannan kuma ta gaji da ba su kudi. Su kuma ganin ba su sami kudin ba ya sanya suka yada wannan bidiyo.

Akwai shaidar takardun banki a kan yadda ta rinka tura musu kudin da suke nema daga wajen ta, saboda haka yanzu muna aiki da jami’an tsaro wajen kama su”. Inji Alhassan Kwalle.

A yanzu dai jami’an tsaro na neman wadandan mutane guda biyu ruwa a jallo, yayin da su kuma suka yi batan dabo.

Haka zalika mun yi yunkurin jin ta bakin jarumar Maryam Booth dangane da wannan batu, amma har yanzu hakar mu ba ta cimma ruwa ba, watakila sai a nan gaba.

#Northflix

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

1 Comment
  1. Anonymous says

    ita tajama kanta

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.