Wasanni

Ana Ci Gaba Da Tona Asirin Shugaban Real Madrid

Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da kalamai marasa dadi da shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez ke fdi a kan wasu daga cikin tsofaffin fitattun ‘yan wasansa da ma ddaya daga cikin masu horaswar da suka yi aiki tare.

Hira ta baya bayan nan da jaridar El Confidencial da ake wallafata a intanet ta bayyana ita ce wadda Perez ke bayyana tsohon mai tsaron ragar kungiyar, Iker Casillas da ddan wasan gaba Raul Gonzales a matsayin wadanda suka yiwa kungiyar Real Madrid damfara mafi muni, hirar da yayi tun a shekarar 2006.

A ranar Laraba jaridar ta El Confidencial ta fitar da wata hirar muryar shugaban na Real Madrid da aka nada da yake yin watsi da kimar tsohon dan wasan kungiyar da babu kamarsa Cristiano Ronaldo da kuma tsohon kocinsa Jose Mourinho.

Cikin hirar da aka nada a shekarar 2012, an jiyo Perez na bayyanawa wani da ba a san ko waye ba cewar Ronaldo maras hankali ne la’akari da wasu irin dabi’unsa na rashin nutsuwa, duk da bajintar da ya yiwa kungiyar Real Madrid daga shekarar 2009 zuwa 2018 ciki har da taimaka mata wajen lashe kofunan gasar Zakarun Turai guda hudu.

Perez ya kuma caccaki Jorge Mendes wakilin Ronaldo da kuma tsohon kocinsu Jose Mourinho wanda ya horas da kungiyar ta Real Madrid a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013 da suka gabata.

Publicité

A cewar Perez Mendes wanda dan asalin kasar Portugal ne ba shi da tasiri ko kadan kanmai koyarwa Jose Mourinho da Ronaldo da yake yiwa dillanci kuma sai abinda suka yanke za suyi a rayuwarsu.

Tuni dai Florentino Perez ya bayyana cewa zai dauki matakin shari’a akan wannan jaridar wadda take bankado wasu maganganun da yayi akan tsoafffin ‘yan wasan kungiyar tun a shekarun baya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: