Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa kasa da kashi 24 bisa 100 na jarirai ne suke samun shayarwar wayen su wato nono na tsawon watanni shida a kasa Najeriya.

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Chimay Thompson ya fadi haka, sannan ya kara da cewa rashin yin haka na daya daga cikin dalilin dake kara mace-macen yara da mata.

” Shayar da yaro ruwan nono zalla na tsawon watanni shida hanya ce dake taimaka wa wajen inganta lafiyar yaro da na uwa.” Inji Thompson.

Sai dai bincike ya nuna cewa haka ba shine yake faruwa ba a kasar nan domin miliyoyin mata basa juriyar shayar da ‘ya’yansu nono na wannan tsawon lokaci.

Ya ce bincike ya nuna cewa shayar da ‘ya’ya nono zalla na tsawon lokaci na taimakawa wajen bada tazarar iyali, rage kiba, kare mace da kamuwa da hawan jini, kara dankon zumunci tsakanin uwa da ‘da.