Hukumar tsaro ta Sibil Difens NSCDC ta musanta batun daukar sabbin ma’aikata da ta ke yi, inda ta ce an yi wa shafin ta kutse.
Mai magana da yawun hukumar, Emmanuel Okeh shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a
Hukumar na gargadin mutane da su yi watsi da duk wani jita jitan da ke nuna cewa suna daukan aiki a yanzu haka, wanda ya bazu a shafuka sada zumunta da labarai na yanar gizo.
Okeh ya gargadi ‘yan Nijeriya da su guji fadawa hannun ‘yan damfara wadanda suka yi kutse a shafin su na yanar gizo domin su cuci ‘yan Nijeria masu neman aiki.
Haka zalika ya yi kira da a yi watsi da wasu sakonni da ke amfani da addini wajen sanya mutane su yi rajistar neman aiki, inda ya kira wannan sako aikin bata gari.
Ya bayyana cewa idan lokaci ya yi da za su dauki sabbin ma’aikata, toh za su wallafa a manyan gidan jarida na kasar nan kuma su tallata a gidajen rediyo da talabijin ba kafofin sada zumunta da yanar gizo ba.
A ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar ta sanar da cewa za ta dauki ma’aikata 3500, sai dai ta ce ba ta samu amincewar gwamnatin tarayya ba tukunna.
Add Comment