Labarai

An Yi Kiira Ga Gwamnatin Jihar Kano Da Ta Duba Matsalar Da Ta Sa Aka Samu Tsaikon Fitowar Sakamakon Jarabawar NECO

Shugaban gidauniyar tallafawa mabuƙata daga tushe wato ‘Grassroot Care & Aid Foundation’ Amb Auwal Muhd Danlarabawa ne ya yi wannan kira dan isar da saƙon dubunnan Dalibai dake makarantun gwamnati a jihar Kano.

Amb Auwal Muhd Danlarabawa yace ya kamata gwamnati tayi iya ƙoƙari wajen ganin an samu sakin sakamakon wannan Jarabawar ta Neco da ta dade bata fito ba, duba ga Jarabawar ta Neco ta daliban makarantu masu Zaman kansu tuni tasu ta fito har sun fara samun damar neman shiga makarantun gaba da sakandare a sassa daban daban da cigaban karatunsu.

Hakan ne yasa daliban da basu samu tasu Jarabawar ba suka nemi da gidauniyar tayi Kira ga gwamnati dan a baya sunji gwamnatin tace ta biya kuɗin da ake buƙata Daga ɓangarenta Amma har yanzu shiru ba labarin fitowar Jarabawar ta Neco na ɗaliban na jihar Kano.

Duba ga wasu dama gwamnatin ce ta taimaka musu da kuma Wanda suka biya da kansu a makarantun da kuma Wanda kungiyoyi na taimakawa mabukata suka biyawa sabida rashin samun kasancewa daga cikin Wanda suka ci Jarabawar kwalifayin.

Muna fatan wannan saƙo zai Kai ga gwamnatin ta jihar Kano tare da sharewa waɗannan yara ɗalibai Yan a salin jihar ta Kano hawayensu, da cimma burinsu da suke dashi na cigaba da karatu a makarantun gaba da sakandare kuma ayi alfahari dasu anan gaba, musanman Dan cike gurbin Nan na Kiran da gwamnatin jihar Kano keyi na kowa yaje makaranta a nemi ilmi abar zaman banza da tunani marasa kyau a unguwanni.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: