An Yi Gagarumar Nasara Kan Boko Haram

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Datti Assalafiy

Da alama mataki na gaba da shugaba Buhari ya tafi yazo mana da babban alheri a yaki da ta’addancin annoba ‘yan kungiyar Boko Haram.

Talla

Abu na farko: Kafin ISIS karkashin jagorancin Abubakar Al-baghdadiy su karbi mubayi’ar tsagin kungigiyar Boko Haram na Habibu Muhammad Yusufa Al-barnawiy sai da ISIS ta ce matukar suna so ta karbi muba’iyar su tabbata sun cika ka’idar yarjejeniya kamar haka:-
-Kwace ikon manyan garuruwa a arewa maso gabashin Nigeria
-Su tabbatar ba’a gudanar da babban zaben kasar Nigeria na shekarar 2019 ba

Idan Boko Haram suka cika ka’idar wannan yarjejeniya to ISIS zata karbi mubayi’arsu ta yanda zata cigaba da basu taimakon kayan yaki, kwararrun mayaka da kudi, amma cikin ikon Allah Boko Haram sun gaza wajen cika ka’idar wannan yarjejeniya da sukayi da ISIS.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Abu na biyu: Tabbas Boko Haram sunyi kyakkyawan shiri don su kaddamar da mummunan harin ta’addanci a garin Maidugurin jihar Borno da garin Geidam na jihar Yobe a ranar da za’a gudanar da zaben shugaban Kasa, don su hana gudanar da zaben a jihohin, amma sai suka hadu da mummunan turjiya daga sojojin kundunbala na Nijeriya.

Inda a ce Boko Haram sun samu nasaran hana zabe a jihohin Borno da Yobe to da burinsu ya cika, ISIS zata gani ta samu kwarin gwiwar cigaba da basu tallafin kayan yaki, mayaka da kudi, don haka da ta bayyana wa ISIS cewa Boko Haram ta gaza wajen cika yarjejeniyar da sukayi da ita to zata janye daga basu tallafi, kunga jama’a Boko Haram zasu kara samun rauni da karayar tattalin arzikinsu ta yanda ba zasu iya cigaba da wanzar da ayyukansu na ta’addanci sosai ba

Cigaban da muka gani a yaki da Boko Haram da sojojin Nigeria sukeyi ya karu tun daga ranar da aka gudanar da zaben shugaban Kasa zuwa yau, duk lokacin da ‘yan ta’addan sukayi yunkurin kaddamar da hari sojoji suna dakilesu ta sama da kasa, mun yaba da matakin NEXT LEVEL, wata babbar nasaran sai shugaba Buhari ya rabu da maciya amanar da suka masa taqiyyah

Muna rokon Allah Ya raba tsakanin shugaba Buhari da maciya amana Amin

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: