An yi finafinai 635 a Nijeriya a kwata ta biyu ta 2021, inji gwamnati

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

- Advertisement -

GWAMNATIN Tarayya ta bayyana cewa masana’antar shirya finafinai ta Nijeriya, wadda ake kira Nollywood, ta samu nasarar ƙara yawan finafinan da ta ke shiryawa a kwata ta biyu ta shekarar 2021 zuwa finafinai 635 daga guda 416 da ta shirya a watanni uku na farkon shekarar.

Wannan bayanin ya na ƙunshe ne a cikin wani rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, (National Bureau of Statistics, NBS) ta fitar a ranar Laraba, wanda mujallar Fim ta samu kwafen sa.

Rahoton, mai taken “Bayanin Shirin Finafinan Nollywood a Kwata ta Biyu ta 2021 (“Nollywood Movies Production Data for Quarter Two, 2021”), an wallafa shi ne a gidan yanar hukumar.

A cewar rahoton, waɗannan alƙaluma na nuni da cewa an samu ƙarin cigaba na kashi 53.93 cikin ɗari daga wannan kwata zuwa waccan kwatar da kuma cigaba na kashi 1.44 cikin ɗari daga wannan shekara zuwa wannan shekara a bisa finafinai 626 da aka shirya a cikin kwata ta biyu ta shekarar 2020.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 904

A nazarin da ta yi na wuraren da ake shirya finafinan, NBS ta ce Jihar Legas ce ta fi ko’ina yawan finafinan da aka shirya, domin kuwa ta yi finafinai 234. Daga ita sai Abuja mai finafinai 196, sai kuma garin Anaca mai finafinai 174.

Garin Jos na da finafinai tara, Kano na da shida, sai Benin da Fatakwal da su ke ɓutal da finafinai bakwai kowannen su.

Hukumar ta ce wajen tattara wannan rahoto, ta samu alƙaluma daga Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB), yayin da ita NBS kuma ta yi nazarin su tare da tabbatar da ingancin su.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa idan aka ce Nollywood, to ana maganar finafinan Nijeriya baki ɗaya ne, waɗanda su ka haɗa da na masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood, ba na ‘yan Kudu kaɗai ba.

Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.