News

An yankewa Abduljabbar Hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.

An yanke hukuncin ne a ranar Alhamis bayan da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce an same da dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su. bbchausa na Ruwaito

Daga cikin tuhumar da ake masa, hadda zargin wa’azinsa zai iya tayar da tarzoma a jihar Kano.

Bayan an same shi da laifukan, sai Mai Shari’a Sarki Yola ya dage zaman kotun don ba shi damar rubuta hukuncin da za a yanke wa malamin.

Bayan dan lokaci kuma sai aka koma zaman kotun tare da yanke hukuncin.

Sai dai kafin a tafi hutun Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya yi magana ta karshe inda ya ce lauyan da ke kareshi bai san shi ba kuma baya neman afuwa saboda a cewarsa bai aikata laifi ba, don haka a gaggauta yanke masa hukunci.

A ranar Juma’a 16 ga watan Yulin 2021 ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Awaisu Al’arabee Fagge shugaban jibwis social media a kano ya kara da cewa

An kwance littattafansa da ya gabatar. Zaa kai littattafan State Library.

Anyi umarnin gwamnatin Kano ta gaggauta kwace masallatan Abduljabbar.

An haramta sanya karatuttukansa da hotunansa a Rediyoyi, Talabijin, Da Shafukan Sadarwa.

Jibwis Social Media
Kano State.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.