AN YANKA TA TASHI: Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta sauya Kawu Sumaila da Dambazau

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babbar kotun tarayya dake jihar Kano ta umarci hukumar zabe da ta karbe shaidar cin zabe da ta mika wa tsohon hadimin Buhari Kawu Sumaila cewa ba shi bane ya cancanta ya zama dan majalisar Tarayya na shiyyar da yake wakilta daga jihar Kano.

Da yake zartar da hukunci a zauren kotun, Alkali Lewis Allagoa ya bayyana cewa jam’iyyar APC bata yi daidai ba musanya ainihin dan takaran da aka yi zaben fidda gwani dashi na jam’iyyar wato babban dan ministan Ayyukan cikin gida, AbdulRahman Dambazau.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 88

Lauyan Dambazau, Nuraini Jimoh ya bayyana cewa tun farko Kawu Sumaila bai tsaya takarar kujerar dan majalisar Wakilai ta Tarayya ba, ya nemi kujerar sanata ne inda suka fafata da Sanata Kabiru Gaya. Kabiru Gaya ne ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar a wancan lokaci. Bayan haka kwatsam sai jam’iyyar ta musanya shi Dambazau da yayi nasara a zaben fidda gwani na APC da Kawu wai domin wai a saka masa.

Dambazau ya garzaya Kotu inda ya kalubalanci wannan shawara da jam’iyyar ta yanke.

Yanzu dai kotu ta umarci hukumar Zabe ta gaggauta kwato shaidar lashe zabe da zama dan majalisa da ta mika wa Kawu sumaila ta ba Dambazau cewa shine zababben dan majalisar da aka zaba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.