A yaune Shafin AREWABLOG ya sami katin daurin auren Sulaiman Isah Isah matashin dake zaune a garin Panshekara dake nan Kano da kuma masoyiyar sa baturiya.
Tun a watannin baya Akaso daura wannan aure amma annobar Corona Virus ta dagatar da wannan abin Alheri inda tasa dole a dage daura wannan aure har zuwa lokacin da wannan annobar zata lafa.
Masoyan guda biyu sun hadune akafar sada Zumunta ta Instagram yayinda wannan baturiya taga hotunan wannan matashi kuma taga yana kaunarsa hakan yasa ta taso tundaga garinsu har zuwa birnin Kano domin yiwa sahibin nata kallon qurilla kuma ta gamsu yadda tasamu tarairaya da kuma kula irin ta masoyi duk da cewa ita wannan matar ta girmi wannan matashi.