An tsaurara tsaro a wajan daza ayi taron rantsar da sabon gwamnan Kano
Dàga Umar Saleh Zara
A cigaba da shirye shiryan rantsar da sabon zababban gwamnan jihar Kano Injiniya ,Abba Kabir Yusuf,hadakar jami’an tsaro sun dira a filin wasa na Sani Abacha a kofar mata dake jihar Kano domin tabbatar da tsaro yayin bikin rantsuwar sabon gwamnan.
Tun ana wajan saura kwanaki bakwai bikin rantsuwar aka jibge jamian tsaro daban daban a filin taron.
A ranar laraba da Alhamis kwamashinan yansandan jihar ta Kano CP Husaini Gume,l da shugaban hukumar tsaron farin Kaya da sauran shugabanin jami’an tsaro suka ziyarci filin daza a gudanar da taron domin ganewa idon yadda lamarin tsaro yake a wurin.
a ranar Alhamis din data gabata kwamashinan yansandan jihar ta kano ya jagoranci faretin girmamawa na gwaji ga zababban gwamnan jihar mai jiran rantsuwa,wanda kwamashinan yace sunyi hakan ne domin sabon gwamnan ya samu sani gami da yadda ake gudanar da faretin kafin ranar rantsuwa.
Tawagar gwamnan mai jiran rantsuwa sun shafe awanni a wajan faretin gwajin daya gudana.
CP Gumail, ya gargardi dukkan wanda ke yunkurin tayar da wata tarzoma a wajan taron akan ya kuka da kansa kuma ya hakura da yunkurin domin baza su saurarawa kowa ba kan hakan domin suna kula da motsin kowa a wurin.
Dakta Dan Yaro Ali Yakasai ,jigo a kwamatin tsaro na karbar mulki ya yabawa kwamashinan yansandan wanda yace tabbas sun gamsu da yadda yake gudanar da aikin sa.
Injiniya Abba Kabir Yusuf daga jami’iyar NNPP ya kayar da abokin kaarawarsa mataimakin gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf, Gawuna daga jami’iyar APC da kuri’u masu rinjaye kamar yadda hukumar zabe ta baiyyana.
Alumma a jihar ta Kano nacigaba da shirye shiryan zuwa bikin rantsuwar dazai gudana a gobe litinin 29-5-2023 wanda zasuyi adon fararan Kaya da jar hula domin yin koyi da jagoran jamiyar NNPP na Kasa,Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Ana ganin taron rantsuwar na Kano yafi na kowacce jiha daukar hankalin alumma.
Zuwa yanzu dai an kayata wajan taron gaagarumin bikin rantsuwar da ado kala kala.
Add Comment