An Soma Fafatawa Tsakanin Atiku Da Buhari

1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ranar Lahadi ne aka buga kugen siyasa a Najeriya inda ‘yan takara a matakin tarayya za su soma yakin neman zaben 2019 gadan-gadan.

Dokokin hukumar zaben kasar, INEC,  sun nuna cewa 18 ga watan Nuwamba 2018 ita ce  ranar da a hukumance za a soma yakin neman zaben.

Talla

Fiye da mutum 30 ne ke takarar shugaban Najeriya, sai dai masana na ganin fafatawar za ta fi yin zafi ne tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP. Dukansu biyu shekarunsu na haihuwa sun wuce 70.

Shugaba Buhari ya ce zai nemi wa’adi na biyu na shugabancin  kasar ne saboda “na kammala ayyukan da na soma.”

Shugaban, wanda ya kayar da Shugaba na wancan Goodluck Jonathan a zaben 2015, ya gina takararsa ne kan abubuwa uku: wanzar da tsaro,  samar da ayyuka da kyautata tattalin arzikin kasar, da kuma yakar rashawa

Masana harkokin tsaro  da dama irinsu Malam Kabiru Adamu sun amince cewa shugaban ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro – musamman a yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta kashe dubban mutane sannan ta raba miliyoyi daga gidajensu.

Tarihin Atiku Abubakar a takaice

 • Shekararsa 72
 • Ya zama gwamnan jihar Adamawa
 • Ya yi mataimakin shugaban kasa 1999 zuwa 2007
 • Hamshakin dan kasuwa ne
 • Ya rike mukami a hukumar Customs
 • Ya sha fuskantar zarge-zargen cinhanci da rashawa
 • Musulmi ne daga arewacin Najeriya

Sai dai sun nuna gazawar shugaban wajen shawo kan matsalolin masu satar mutane don karbar kudin fansa da rikicin namona da makiyaya – wadanda suka yi kamari a shekarun baya bayan nan.

Kazalika an sha caccakar Shugaba Buhari saboda gaza yin tagomashi kan inganta tattalin arzikin Najeriya, ko da yake gwamnatinsa ta sha cewa zai dauki lokaci kafin kasar ta warke daga masassarar tattalin arzikin da ta fada a ciki lokacin da ta karbi mulki, kamar yadda ministar kudi Zainab Ahmed ta jaddada a hirar ta da BBC a makon jiya.

Tarihin Muhammadu Buhari a takaice

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86
 • Shekararsa 76
 • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
 • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1983 zuwa 1985
 • An hambare shi a juyin mulki
 • Kungiyoyin kare hakkin dan adam na zarginsa da kin bin umarni kotu
 • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
 • Musulmi ne daga arewacin Najeriya

Sake gina Najeriya 

A nasa bangaren, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin sake gina Najeriya ta hanyar warware matsalolin tattalin arzikin da take ciki.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya ce ya kware wajen kasuwanci da samar da ayyuka, ya yi alkawarin sama wa matasa ayyuka da inganta tsaro.

Sai dai gwamnatin Buhari da magoya bayanta sun sha sukar Atiku Abubakar wanda suke zargi da cinhanci da rashawa, zargin da yake musantawa.

A matakin jihohi, wata kididdiga da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa mutum 821 ne ke takarar gwamna a jiha 28 da za a gudanar da zabe. Nan gaba ne dai za a soma yakin neman zaben gwamnoni.

INEC ta gargadi masu takara a dukkan matakai kan tsaftace kalamansu lokacin yakin neman zabe tana mai yin alwashin duk wanda ya keta dokokinta.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: