-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

An Sanya Dokar Ta Baci A Unguwanni Biyar Dake Jihar Bauchi


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An Sanya Dokar Ta Baci A Unguwanni Biyar Dake Jihar Bauchi

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya dokar hana walwala daga 6 na safe zuwa 7 na yammaci a wasu unguwanni biyar da aka samu rahoton rikici.

A wata sanarwa da mai taimakawa Gwamnan jihar Bauchi a fannin sadarwa, Shamsudeen Lukman ya fitar a safiyar ranar Laraba, ya ce Gwamna M.A Abubakar ne ya sanar da sanya dokar a hirar da ya yi da manema labaru a fadar Gidan Gwamnati.

Majiyarmu ta ruwaito unguwannin da dokar ta shafa sune Yelwa Tsakani, Lushi, Unguwar Kusu, Unguwar Ngas da kuma Kagadama.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai wata takaddama ta barke tsakanin wasu gungun matasa a yayin da suke yin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar dayansu a unguwar Yelwa Tsakani da Lushi lamarin da ya juye zuwa rikici har ta kai ga an rasa rayuka uku tare da kona gidaje biyu.

Sanarwar tace sanya dokar ya biyo bayan da aka samu rahoton matasan sun takali yansandan kwantar da tarzoma da aka tura yankin domin kwantar da rikicin.

Gwamnan yace dokar zata cigaba da ci har zuwa lokacinda abubuwa suka daidaita a unguwannin.

Gwamnan ya yi kira da a cigaba da zaman lafiya a jihar domin samun cigaba mai dorewa.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: