Uncategorized

An samu raguwar mutuwar mata masu ciki

Image copyrightPA
Image caption
An samu raguwar mace-macen mata masu ciki.
Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya sun ce mace-macen mata da ke da alaka da haihuwa sun ragu da rabi tun daga shekara ta 1990.
Sai dai kasashe tara ne kawai suka cimma adadin da majalisar dinkin duniya ta shata na Muradin Karni.
Amerika tana cikin kasashe goma sha uku na duniya da lamarin ya kara muni a cikin shekaru ashirin da biyar da suka wuce.
Yiwuwar matan su mutu sanadin haihuwa ya fi yawa a Amurkar har linki biyu fiye da Kanada.