Kannywood

An Samu Miliyoyin Kudi A Wajan Kallon Fim Din Tsakaninmu

Fim din TSAKANIN MU ya haɗa kuɗi Naira Miliyan Uku da Dubu Ɗari Biyu da Casa’in da Takwas da Ɗari Biyar (₦3,298,500) a cikin sati biyu.

Wannan babbar nasara ce, duba da fim din ya futa ba lokacin hutu ba, kuma adaidai lokacin da sinima take cikin zazzaɓi na rashin makallata sakamakon wakaje wakazo da ake tayi da hankalin ƴan kallo sabo da cutar Coronavirus, dukda fim din ya samu tagomashin karin farashin tikitin shiga kallo sabanin sauran finafinan.

Fim din #tsakaninmuthemovie ya shiga jerin finafinan da suka haɗa kuɗi masu nauyi acikin sati biyu, wanda hakan alama ce da take nuna fim ya samu karbuwa a wajen yan kallo, kuma shi yake nuna girma da isa ta su masu film din (Producer & Director).

TOP 5 KANNYWOOD GROSSERS IN TWO WEEKS

1. MATI A ZAZZAU – ₦4,489,400
2. HAUWA KULU – ₦3,562,000
3. KARKI MANTA DANI – ₦3,474,100
4. TSAKANIN MU – ₦3,298,500
5. BANA BAKWAI – ₦3,180,000

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: