Allah ya kubutar da Zainab Hussain Maitsani wadda masu garkuwa da mutane suka dauka a gidan kakanta wato ALH. HUSSAIN MAITSANI shugaban jam’iyar PDP na karamar hukumar Dutsinma ranar Laraba 28-11-2018.
An karbo Zainab ne akan kudi naira milyan uku (3000,000) lakadan ba ajalan ba. Inda yanzu haka tana gida kuma tana cikin koshin lafiya.
- Advertisement -
‘Yan uwan ta sun mika godiyar su ta musamman ga dimbin ‘yan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa akan addu’o’i da suka taya su.
Daga Mustapha Samaila Dutsinma