-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

An Saki Sabin Bidiyon Karbar Rashawar Kashi Na 6


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: AN SAKI SABON FAI-FEN BIDIYON KARƁAR RASHAWA KASHI NA 6.

“GWAMNA GANDUJE KA ROƘI AFUWAR MA’AIKATAN DA KA KORA AIKI, ALHAKIN SU KE BIBIYAR KA”

Ƙasa da mako ɗaya da Babbar Kotun kano tayi hukuncin hana ɗan jarida Jaafar Jaafar da Kamfaninsa DailyNigeria sakin wani sabon faifen bidiyo mai nuni da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje OFR, Khadimul Islam yana karɓar kuɗaɗe da ake zargin rashawa ce daga hannun wani ɗan Kwangila, ayau sai gashi wani sabon bidiyon ya sake ɓulla.

A wannan sabon bidiyo, anji mai bada kiɗin yana maganar rumfunan Kantin Kwari ne, da kuma wasu raguwar kuɗi da Akanta Janar bata gama biyan su ba.

Babu tabbacin wanda ya fitar da bidiyon.
Amma dai, tana iya yiwuwa hakan bata rasa nasaba da ƙara kusantowar siyasa domin kada hankulan mahukunta ya bar kan lamarin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 15

- Advertisement -

Wasu masu fashin baƙi kuwa sun shiga baiwa Gwamna Ganduje shawarar ya gyara kuskuren da Gwamnatinsa ƙarƙashin shugaban ma’aikata Auwal Na Iya tayiwa ma’aikatan lafiya, wadda ta kora bisa zargin rashawa bayan anyi musu aringizon albashi.

A cewar su wannan ɓullar faifen bidiyo alhakin su ne.

Wata majiya daga majalisa ta faɗi cewar tuni majalisa ta bada Umarnin Shugaban ma’aikatan yayi gaggawar mayar da ma’aikatan bakin aikinsu, Gwamnan ma da kansa yayi wannan umarnin amma duk a banza, domin shugaban ma’aikatan yaƙi bin umarnin.

https://www.youtube.com/watch?v=AM6X1S9EAbw

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: