Labarai

An Sace Sarki Da Iyalansa Mutum 12 A Kaduna

Daga Sulaiman Ibrahim
‘Yan bindiga sun sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu a fadarsa da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

‘Yan fashin sun kuma tafi da wasu ‘yan uwansa 12, ciki har da mata da yara.

Jikan sarki kuma mai rike da sarautar ‘Dan Kajuru’, Saidu Musa, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Jaridar Daily Trust.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na safe.

Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, da Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan sanda, Jalige Mohamed, ba su amsa kiran tarho da akayi musu ba a lokacin rubuta rahoton.

Duk, da cewa, ‘yan bindiga sun dade suna azabtar da mazauna Jihar Kaduna, amma ‘yan satinkan nan, lamarin ya ta’azzara sosai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: